Nijar : Sojoji Sun Kwace Daukacin ikon Bosso da Kuma Kewayensa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6523-nijar_sojoji_sun_kwace_daukacin_ikon_bosso_da_kuma_kewayensa
Rahotanni daga Nijar na cewa garin Bosso da kuma kewayensa, ya koma karkashin ikon rundinar sojin kasar, bayan shafe kwanaki na tabbatar da tsaro a yankin tare hadin gwiwar rindinar sojin saman Chadi, karkashin jagorancin kwamanda janar Ahmed Mohamed, mukadashin babban hafsan sojin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 10, 2016 06:42 UTC
  • Nijar : Sojoji Sun Kwace Daukacin ikon Bosso da Kuma Kewayensa

Rahotanni daga Nijar na cewa garin Bosso da kuma kewayensa, ya koma karkashin ikon rundinar sojin kasar, bayan shafe kwanaki na tabbatar da tsaro a yankin tare hadin gwiwar rindinar sojin saman Chadi, karkashin jagorancin kwamanda janar Ahmed Mohamed, mukadashin babban hafsan sojin kasar.

Wannan dai ya zo bayan mumunan hari da 'yan ta'adan boko haram suka kai a garin na Bosso a ranar Juma'a data gabata, wanda yayi sanadin mutuwar sojojin kasar 26 tare da raunana sama da 100.

Tuni dai hukumomin yankin da sarakunan gargajiya sukayi kira ga al'umma dasu koma gidajen su.