Faransa Ta Jadda Anniyarta ta Kare Lafiyar Fararen Hula A Nahiyar Afrika
Faransa Ta Bukaci A Kare Lafiyar Fararen Hula A Nahiyar Afrika
Kasar faransa wacce take shugabancin komitin tsaro na majalisar dinkin duniy a wannan watan ta bukaci sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a wasu kasashen Afrika su yi kokarin kare fararen hula na wadan nan kasashe daga fadawa cikin hatsari.
A zaman komitin tsaron na jiya jumma'a wanda ya sami halattar ministan harkokin wajen kasar ta Faransa , shugaban komitin ya jaddada bukatar kare lafiyar fararen hula a kasashen da sojojin majalisar suke aiki, musamma a kasar Afrika ta tsakiya da kuma Mali.
Wasu labarai da aka yada na baya bayan nan sun nuna wurare 44 wadanda sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya suka ci zarafin yara kanana. Majiyar ta kara da cewa 29 daga cikin wadan nan wurare sun faru ne a kasar Afrika ta tsakiya.