Fada Da Ta'addanci A Afirka Ta Tsakiya:
Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddawa Wajabcin Fada Da Ta'addanci A Kasar Afirkata ta tsakiya.
Wasu mambobin kwamitin shawar na majalisar dinkin duniya akan harkokin tsaron kasar Afirka ta tsakiya sun jaddada wajabcin ci gaba da fada da ayyukan ta'addanci.
Kwamitin mai mutane 11 da su ka yi wani taro a jiya juma'a a birnin Bongui a jiya juma'a, sun jaddada muhimmancin ci gaba da fuskantar ayyukan ta'addanci.
Jakadan kasar Kamaru a Afrika ta tsakiya Nicolas Nzoyoum ya yi ishara da manufofin da aka yi aiki da su wajen fada da kungiyar Bokoharam, ya bukaci samun cikakken hadin kan dukkanin mambobin kwamitin domin fada da ta'addancin.
Ministan harkokin wajen kasar Gabon Moungara Moussoti wanda memba ne a cikin kwamitin ne ya karanta bayanin bayan taron, inda a cikin ya nuna jin dadinsa dangane da ci gaban da ake samu ta fuskar tsaro a kasar.