Tattaunawar Sulhu A Burundi
'Yan hamayyar Siyasar Kasar Burundi sun nuna amincewarsu da shiga tsakanin tsohon shugaban kasar Tanzania.
A yau asabar ne aka yi ganawa a tsakanin tawagar 'yan hamayyar kasar ta Burundi da kuma tsohon shugaban kasar Tanzania, Benjamin Mkapa a birnin Brussels na Belgium.
Tawagar ta Burundi ta yabawa Mkapa akan rawar da ya ke takawa ta shiga tsakani tare da nuna gamsuwarsu da shi.
Mai magana da yawun 'yan hamayyar kasar ta Burundi Jeremie Minani ya fadi cewa; Ganawar da su ka yi da tsohon shugaban kasar ta Tanzania wata nasara ce a gare su, domin kuwa yana a matsayin amincewa da kuma yarda da kawancen yan hamayyar ne.
Burundi ta tsunduma cikin rikicin siyasa tun bayan da shugaban kasar Peer Nkrunziza ya yi tazarce.