Bukatar taimakon gaggawa ga 'yan gudun hijrar Nijer
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci taimakon gaggawa ga 'yan gudun hijra a kudu maso gabashin jumhoriyar Nijer.
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Fawzia Daily babbar Jami'a dake kula da harakokin aiyukan Jin kai ta MDD a kasar Nijer, ta yi kira da babbar murya ga kungiyoyin kasa da kasa kan su gaggauta kai dauki ga Mutanan garin Bosso na jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar da rikicin boko haram ya raba da mahalinsu.
Jami'ar ta ce 'yan gudun hijrar na Bosso na cikin mayuwacin hali na rashin ruwa da abinci ,kuma matukar ba a kai musu agajin gaggawa ba, da dama daga cikin su na iya rasa rayuwarsu.
Har ila yau Jami'ar ta kara da cewa matukar kungiyoyin kasa da kasa ba su dauki wannan matsala da mahimanci ba, lamarin na iya shafar yankunan dake yankin tabkin Tchadi, kuma matsalar na iya daukan dogon lokaci kafin a magance ta.
A makun da ya gabata ne mayakan boko haram suka kai mumunar hari a garin Bosso inda suka kwace shi na tsahon sa'o'i kafin daga bisani Dakarun tsaron Nijer su sake kwato shi daga kungiyar boko haram din, a wannan Hari Sojojin Nijer 26 da kuma na Nigeriya 2 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu kimanin 100 na daban suka jikkata.