Faransa Ta Bugaci A Tura Yansanda Zuwa Kasar Burunda
Gwamnatin kasar Faransa ta bukaci kasashen duniya su tura yansanda zuwa kasar Burundi don tabbatar da zaman lafiya a kasar. Sahafin yanar gizo na labarai "Africa Time " ya nakalto majiyar gwamnatin kasar Faransa tana bayyana haka a yau jumma'a.
Gwamnatin kasar Faransa ta bukaci kasashen duniya su tura yansanda zuwa kasar Burundi don tabbatar da zaman lafiya a kasar. Sahafin yanar gizo na labarai "Africa Time " ya nakalto majiyar gwamnatin kasar Faransa tana bayyana haka a yau jumma'a. Ta kuma kara da cewa bayan kudurin da majalisar dinkin duniya ta samar kan rikicin kasar na Burundi a cikin watan Newamba na shekara da ta gabata, ana saran nan ba da dadewa ba komitin tsaro na majalisar zata zauna don ganin an tura jami'an yansanda wadanda zasu yi aiki tare da sojojin kasar ta Burundi don tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Labarin ya kara da cewa yansanda da zasu tura zasu yi aiki tare da sauran Jami'an tsaro na kasar Burindi sannan ta haka za'a gano yansandan kasar wadanda suke kunna wutan fitana ta hanyar kashe masu adawa da shugaban kasar Pierre Nkurunziza.