Nijar : 'Yan Ci Rani 34 Sun Mutu A Hamada
-
Ko a bara dai, \'yan ci rani 33 sun mutu a hamadar Sahara
A Jamhuriya Nijar 'yan ci rani 34 ne, suka rasu a kokarin ketara hamada don shiga kasar Aljeriya.
Wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar a Jiya ta ce mutanen da suka mutu sun hada da maza biyar, mata tara, da kuma yara 20.
Sanarwar ta ce mutanen dai sun mutu ne tsakanin ranar 6 zuwa 12 ga wannan watan, bayan da masu fasakwaurinsu suka yi watsi dasu.
Wata majiya tsaro ta shaidawa kanfanin dilancion labaren AFP cewa, an gano gawawakin mutanen ne kusa da ''Assamaka'' dake iyaka kasashen biyu, kuma bisa ga dukkan alamu kishirwa ce ta kashe su.
Kawo yanzu dai an kai ga tantance gawawakin mutane biyu da suka hada da wani dan Najeriya da kuma 'yar Nijar guda mai shekaru 26 a cewar kuma sanarwar.
A cewar dai hukumar kula da kwaran bakin haure ta duniya, Nijar ta kasance daya daga cikin kasashe dake zamen wata hanya da bakin haure ke amfani da ita domin kwarara Turai, inda kashi 60% na bakin hauren dake katarawa ta Libya domin shiga Turai a tekun Bahar-Rum sun biyo ne ta Nijar.
Wannan al'amari dai ya kasance babban kalubale ga kasar ta Nijar data ce tana bukatar tallafin kudade daga kungiyar tarayya turai domin dakile wannan matsala.