Iran Ta Kai kara Amurka Kotun Duniya
Jun 16, 2016 00:56 UTC
-
Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani
Iran ta kai kara Amurka a koyun duniya, saboda kin sakin mata wasu kudaden ta da Amurka tayi.
Hakan dai ya biyo bayan da Amurka ta ce zata rike kudin domin biyan diyya ta $ Bilyan biyu ga wasu iyalai Amurkawa da wani hari ya rusa dasu a Beryrut,
Amurka dai na zargin Iran da hannu a wani harin na ranar 23 ga watan oktoba na 1983, batun da Iran ta jima tana musuntawa.
Akan hakan Jamhuriya musulinci ta Iran a cewar shugaba Hassan Rohani, ta shigar da kara Amurka gaban kotun ta kasa da kasa akan satar kudaden ta, kuma Iran zata ci gaba da wannan gwagwarmaya har sai ta cimma bukatar ta.
Shugaban Rohani ya bayyana a Jiya laraba cewa hanyar da kotinan Amurka suka bi ta sabawa doka.
Tags