An Gano Wani Akwatin Nadar Bayannan Tukin Jirgin EgyptAir
Kwamitin dake gudanar da bincike kan musababbin faduwar jirgin EgyptAir ya sanar da gano daya daga cikin akwatinan nadar bayyanan jirgin daya nutse a tekun Bahar-Rum a watan Jiya.
Masu binciken sun ce an fitar da akwatin nadar bayanan wanda yayi raga-raga, aman anyi nasara fitar da bangaren akwatin dake ajiye bayanan, wanda shi ne mafi mahimmanci.
Dama kafin hakan hukumomin kasar masar sun sanar da gano wasu daga cikin tarkacen jirgin da ya yi hatsari a ranar 19 ga watan Mayu daya gabata a tekun Mediterranean dauke da mutane 66 bayan tashin sa daga Paris zuwa birnin Alkahira.
Samun wannan akwatin nadar bayanan zai taimaka matuka wajen gano musababbin faduwar jirgin.
Fasinjojin da hadarin ya rutsa dasu sun hada da ‘yan Egypt 30 da Faransa 15, sai kuma wasu ‘Yan Iraqi guda biyu da Canada biyu da kuma yan kasashen Algeria da Birtaniya da Portugal da Saudiya da Chadi da Sudan.