Nijar : Al'umma Bosso Na Cikin Matuka Damuwa, Inji Bazoum
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6829-nijar_al'umma_bosso_na_cikin_matuka_damuwa_inji_bazoum
'Yan gudun hijira a garin Bosso dake kudu maso gabashin Jamhuriya Nijar na cikin matukar damuwa tun bayan kazamin harin da 'yan ta'adan boko haram suka kai a yankin a cewar ministan cikin gida na kasar Bazoum Mohammed.
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 16, 2016 13:52 UTC
  • Ministan cikin gida na Nijar, Bazoum Mohammed
    Ministan cikin gida na Nijar, Bazoum Mohammed

'Yan gudun hijira a garin Bosso dake kudu maso gabashin Jamhuriya Nijar na cikin matukar damuwa tun bayan kazamin harin da 'yan ta'adan boko haram suka kai a yankin a cewar ministan cikin gida na kasar Bazoum Mohammed.

Bazoum ya bayyana hakan ne yau Alhamis a wata ziyara daya kai yankin, inda a cewar sa al'umma na cikin zullumi, duk da cewa yanayin rayiwa ya fara daidaituwa tun bayan harin na ranar 3 ga watan nan.

Minista Bazoum wanda ke jayeda wata babbar tawagar ministoci da jami'an kungiyoyin na MDD da masu zamen kansu, ya kai ziyara a sansanin 'yan gudun hijira na Diffa.

Alkalumen da Mdd ta fitar sun nuna cewa adadin 'yan gudun hijira ya karu matuka saboda mumunan harin 'yan boko haram din na baya bayan nan wanda yayi sanadin mutuwar sojojin kasar ta Nijar 24 da kuma na Najeriya biyu.

kafin hakan dai mdd ta ce, za a ninka agajin abincin da ake bai wa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu a jamhuriyar ta Nijar bayan harin da ya tilasta wa mutane kusan dubu 50 kaurace wa muhallansu.

Mdd ta ce babban kalubalen da ke gabanta shi ne, rashin isashen kudi don tallafa wa wadannan mutane da yanzu haka, ko matsugunin kirki basu da shi, sannan wasu ma a bakin hanya suke zama.