An yankewa Tsohon Shugaba Masar Hukuncin daurin rai da rai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6904-an_yankewa_tsohon_shugaba_masar_hukuncin_daurin_rai_da_rai
Kotu ta yankewa tsohon Shugaban kasar Masar Muhamad Morsi daurin rai da rai
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 18, 2016 10:54 UTC
  • An yankewa Tsohon Shugaba Masar Hukuncin daurin rai da rai

Kotu ta yankewa tsohon Shugaban kasar Masar Muhamad Morsi daurin rai da rai

Kotun ta ce ta yanke hukuncin ne kan Morsi da mutum biyu bayan ta same su da laifin yi wa ƙasar Qatar leƙen asiri a lokacin da yake kan karagar mulki.

Kazalika, kotun ta yankewa wasu mutane shida, 'yan ƙungiyar 'yan Uwa Musulmi hukuncin kisa a kan irin wannan laifi, daga cikin su har da Ibrahim Halal da Ala'a Sailan 'yan jaridu biyu na tashar Telbijin din Aljazira ta kasar Qatar.

A baya dai an yanke masa hukuncin kisa da na ɗaurin rai-da-rai.

Bayan yanke wannan hukunci tawagar lauyoyin tsohon shugaban Mursi da sauran Mutananan da aka yankewa hukuncin sun bayyana cewa za su daukaka kara, kamar yadda Kotun ta bawa Morsi din damar daukaka kara idan bai gamsu da wannan hukuncin da aka yanke masa ba.

An yanke wannan hukunci ne a daidai lokacin da ƙasar ke shan suka daga ƙasashen duniya saboda keta hakkin bil adama.

Idan ba a manta ba Shugaba Morsi Shi ne mutumim da ya lashe zaben shugabancin kasar na mulki Dimokradiyya a karon farko tun da aka kawar da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011 sakamakon boren da 'yan kasar suka yi.wanda kuma aka hamɓarar da shi daga kan karagar mulki a watan Yunin shekarar 2013 bayan tarzomar da aka yi a kasar.