Ziyarar shugaban Nijar a Jamus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6916-ziyarar_shugaban_nijar_a_jamus
Jamhuriyar Nijar tayi akawarin bayar da hadin kai wajen magance matsalar kwararar bakin haure daga Afirka zuwa nahiyar Turai.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 18, 2016 13:30 UTC
  • Ziyarar shugaban Nijar a Jamus

Jamhuriyar Nijar tayi akawarin bayar da hadin kai wajen magance matsalar kwararar bakin haure daga Afirka zuwa nahiyar Turai.

A yayin ziyarar aiki na sa'o'i 48 a birnin Berlin na kasar Jamus ,Shugaban Jamhuriyar Nijar Alh Mahamadou Issoufou ne ya bayyana cewa za su yi kokarin samo mafita dangane da batun bakin hauren da ke biyowa ta Jamhuriyar ta Nijar a hanyarsu na zuwa kasashen Turai.

Shugaba Issoufou "Shugabar gwamnatin Jamus ta nunar da cewa a duk shekara sama da bakin haure 100.000 ke biyo wa ta Nijar su shigo Turai. Za mu muyi iya kokari wajen shawo kan matsalar 'yan gudun hijira da ga Libiya. Tarayyar Turai na son shawo kan matsalar Libiya, amma a yanzu Libiya na cikin mawuyacin hali.

A nata jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Jamus za ta tallafawa Nijar kan batun ilimin yara mata tana mai cewa:

"Nijar na da al'umma mai tarin yawa, mun tattauna kan ilimin 'ya'ya mata. A ganina wannan babbar matsala ce. Haka batun tattalin arziki da ma na daina aurar da yara kanana. Muna son mu taimaka matuka da shirinmu na raya kasa."

Issoufuo ya koka kan matsalar rashin tsaro da kasar ta samu kanta sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram, inda ya nemi tallafin kasashen Turai a kan tsaron, yana mai cewa tsaro ba zai tabbata ba sai da ci-gaba kuma babu ci-gaba in har ba bu tsaro.