Take Hakkin Bil'adama A Kasar Burundi
Majalisar Dinkin Duniya Ta Zargi Burundi Da Take Hakkin Bil'adama.
Wasu kwararru na majalisar dinkin duniya sun yi damuwa akan tabarbarewar hakkin bil'adama a kasar Burundi.
Kafar watsa labaru ta Afirca Time ta ambato wasu kwararru na majalisar dinkin duniyar da su ka kai ziyara kasar Burundi, suna fadi a jiya asabar cewa: A cikin wannan kasar babu 'yanci kuma ana iya ganin yadda ake take hakkin bil'adama a ko'ina.
Kwararru da su ka fitar da wani rahoto bayan ziyarar gani da ido a Burundin sun kuma nuna damuwarsu akan hatsarin da ke tattare da kyale al'amurra su ci gaba da tafiya a haka, tare kuma da yin kira ga kungiyoyin fararen hula na kasar da su zage damtse wajen daidaita lamurra.
Kwararrun na majalisar dinkin duniyar sun isa kasar ne ta Burundi a ranar 13 ga watan nan na yuni a karo na biyu, bayan da a karon farko su ka je kasar a cikin watan Maris.
Burundi ta tsunduma cikin rikicin siyasa tun a watan Aprilu na 2015.