Wajibi ne a Karfafa Gwamnatin Afirka ta tsakiya
(last modified Wed, 22 Jun 2016 05:21:58 GMT )
Jun 22, 2016 05:21 UTC
  • Wajibi ne a Karfafa Gwamnatin Afirka ta tsakiya

MDD ta bukaci Gwamnatin Afirka ta tsakiya da ta dauki kwararen matakai a tafiyar da ikon kasar

Bayan kamala ziyarar aiki ta birnin Bangui, Madam Marie-Thérèse Keita Bocoum ma'aikaciyar MDD a bangaren kare hakin bil-adama ta bukaci da a gaggauta karbe makamai daga hanun kungiyoyin dake da dauke da makamai a kasar Afirka ta tsakiyan.

Madam Marie-Thérèse Keita Bocoum ta ce wajibi ne Gwamnati ta dauki kwararen matakai da su farfado da ikonta a tsakanin Al'ummar kasar, Har ila yau Jami'ar ta ce a yanzu ta fahimci damuwar da kungiyoyin kasa da kasa ke nuna na take hakin kananan Yara da Mata a kasar.

Madan Marie-Thérèse Keita Bocoum ta kara da cewa wajibi ne Gwamnatin Afirka ta tsakiyan tare da hadin gwiwar Dakarun kasa da kasa sun dauki kwararen matakai domin karfafa Ikon Gwamnati da kuma kawo karshen rikici.

Wannan ziyara ta Jami'ar MDD na zuwa ne bayan wani sabon rikici da ya yi sanadiyar mutuwar uku a birnin na Bangui.

Sabon rikicin na zuwa ne bayan sace wasu ‘Yan sanda shida a makon jiya. Wannan ya sa ake hasashen cewa ko an yi musayar wuta ne tsakanin ‘Yan sanda da mayakan Seleka.

Rahotanni sun ce daruruwan mutane suka bar gidajensu bayan barkewar rikicin a unguwar da mafi yawanci musulmi ne a birnin na Bangui.

Shaidun gani da ido sun ce an yi amfani da manyan makamai da bindigogin da ke sarrafa kan su.