Wata Tawagar Tarayyar Afirka Ta Kai Ziyara A Burundi
tawagar kungiyar tarayyar Afirka wadda ta kunshi mutane 15 ta isa birnin Bujumbura fadar mulkin kasar Burundi.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoto daga birnin Bujumbura cewa, wannan tawaga ta hada mambobin kwamitin tsaro na kungiyar tarayyar Afirka ne, kuma za su gana da shugaban kasar Pierre Nkurunziza, da kuma wasu daga cikin manyan 'yan siyasa na bangaren adawa a kasar.
Lazare Makayat Safouesse daya ne daga cikin mammbobin wannan tawaga, ya yi wa manema labarai karin haske da cewa, manufar ziyarar tasu dai ita ce kokarin ganin an samu daidaito da fahimtar juna ta fuskar siyasa a kasar, wanda hakan shi kadai ne hanyar samun tabbataccen zaman lafiya a kasar.
Tun bayan zabukan watan Afirilun 2015, kasar Burundi take ta kara tsunduma a cikin matsaloli na siyasa.