Nijar : An Daure Dan fara Hula Saboda Tofa Albarkacin Baki
Wata kotu a jamhuriya Nijar ta yanke hukuncin daurin talala na watanni shida ga mai fafutukar kare demukarradiya da hakin bil'adama nan Abdul Usmane Moumouni daya tofa albarkacin bakinsa a shafinsa na facebook game da yadda gwamnatin kasar ke yaki da kungiyar Boko Haram.
ko baya ga daurin kotun ta ce za'a ci tarar mitinim jikka 50 na kudin CFA.
Bayan dai wannan hukuncin da kotu ta Yamai ya yanke jiya Alhamis, babbar jam'iar kamfe ta kungiyar Amnesty International a yammacin Afrika
Mme Kiné Fatim Diop ta bayyana cewa wannan yana nuna yadda incin fadar albarkacin baki ga 'yan kasar ta ke son kasancewa mai wuya, duba da yadda ake hukunta mutane saboda fadar albarkacin baki akan shafukan sada zumunta wanda kuma zai kasance mumunan makoma ga kasar ta Nijar.
Shi dai Abdul Usman na kungiyar fara hula ta CDDH kana mamba a gamayar kungoyoyin fara hula na Sauvon le Nigare ya rubuta wasu kalamai a shafin sada zumunta na Facebook kan shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou game da yakin da kasar ke yi da mayakan kungiyar Boko Haram, jim kadan bayan harin da suka kai a garin Bosso dake kudu maso gabashin kasar.