Kashe Memebobi Biyu Na Jam'iyyar Da Ta ke Mulki A Burundi
An Kashe Mutane Biyu Masu Kusanci Da Jam'iyyar da ta ke mulki A kasar Burundi A jiya da dare.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato wani jami'in tafiyar da mulki a garin Kiszy da ke tsakiyar kasar ta Buurndi yana fada a yau asabar cewa; Wasu mutane dauke da makamai sun kashe matasa biyu a cikin garin, wadanda su ke da alaka da jam'iyyar da ke mulki.
Selistine Singirankobo ya ci gaba da cewa matasan da aka kashe din suna cikin wata kungiya ce mai damfare da jam'iyyar shugaba Pieer Nkurunziza da ke mulki a kasar.
A cikin wannna watan na Febrairu kadai, an kashe mutane 5 a cikin babban birnin kasar Bujumbura tare kuma da jikata wasu 50.
A cikin watan Aprilu na 2015 ne kasar Burundi ta fada cikin rikici bayan da shugaba Nkrunziza ya yi tazarce.