Za a Tura Akwatin Nadar Bayanai na Jirgin Masar zuwa Faransa
Kasar Masar Ta ce Za ta tura Akwatin Nadar Bayyanai na Jirgin Masar din da aka gano zuwa Kasar Faransa
Kwamitin bincike na Jirgin Fasinjan Masar din da ya fadi ya bayyana cewa a Makun gobe Akwatin nadan bayyanan fasinja da kuma Na'urar nadar bayyanai na dakin Matukan Jirgin samar da aka gano za a tura su kasar Faransa domin gyara su.
Kwamitin ya ce da zarar an kamala gyransu za a dawo da su kasar Masar domin gudanar da bincike a Ma'aikatar bincike na jiragen kasar.
Jirgin Fasinjan na kasar Masar Sanfarin A320 ya fadi ne a yayin da ya fito daga birnin Paris kan hanyarsa zuwa Birnin Alkahira inda dukkanin Fasinjansa dake cikinsa suka hallaka daga cikin su a kwai Misrawa 30 da kuma 'Yan kasar Faransa 15.
A yayin binciken farko Dakarun Kasar Masar Sun sanar da gano wasu kayayyakin Fasinjan da kuma wasu guraguzan Jirgin a ruwan Meditaraniya a kimanin Kilomita 290 daga arewacin Garin Eskandariya na kasar Masar.