Masar ta kare kanta a kan tsibirai biyun da ta baiwa Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7321-masar_ta_kare_kanta_a_kan_tsibirai_biyun_da_ta_baiwa_saudiya
Gwamnatin Masar ta kare kanta kan matakin da ta dauka na baiwa kasar Saudiya wasu tsibirai guda biyu
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 27, 2016 06:00 UTC
  • Masar ta kare kanta a kan tsibirai biyun da ta baiwa Saudiya

Gwamnatin Masar ta kare kanta kan matakin da ta dauka na baiwa kasar Saudiya wasu tsibirai guda biyu

A zaman kotun da ya gudana ranar Lahadin da ta gabata, Lauyen dake kare Gwamnatin Masar ya ce wadannan tsibirai guda biyu mallakin Gwamnatin Saudiya ne a baya, sai Gwamnatin Masar ta ga ya dace da mayar mata da su.

A zaman kotun masu Adawa da matakin Gwamnatin sun yi ta rera take alawadai ga firicin lauyen Gwamnatin.

Wasu 'yan kasar na ganin cewa Gwamnatin ta Masar ta karbi makudan kudade a hanun Sarkin Saudiya Salman bn Abdul-aziz a madadin tsibiran Sanafir da Tiran,

Duk da irin matsin lambar da Shugaba Alsese yake fuskanta na ya yi watsi da matakin da ya dauka da baiwa Saudiyan shibirain kasar, amma ya kauda kai sai ma dai kokarin kare kansa da yake na cewa hakin saudiya ne ya mayar musu.

Gwamantin ta Masar ta ce a shekarar 1950 Gwamnatin Riyad ta bayar da wadannan tsbirai guda biyu ga kasar amana domin amintuwa daga mamayar haramcecciyar kasar Isra'ila.

A yayin yakin 1967 HKI ta mamaye wadannan tsibirai guda biyu, amma bayar yarjejjeniyar sulhu tsakanin Masar da Isra'ilan a shekarar 1979, an mayar wa kasar ta Masar wadannan tsibirai.

A shafinkan yanar gizo, 'yan kasar Masar din na siffata shugaban kasar ta su a matsayin maci amana mai sayar da kasa.