An bukaci Ministan Ilimin kasar Masar Ya yi Murabus
Dubun Daliban Makarantar Sakandare na Masar ne suka gudanar da zanga-zanga ta neman a sauke ministan ilimin kasar daga kan kan mikaminsa.
Dubun dubatan Daliban Makarantar Sakandare na Masar tare ma'aifansu suka yi tsuntsurundu a gaban Ma'aikatar ilimin kasar a yau inda suka nuna rashin amincewarsu da matakin da ma'aikatar ta dauka na soke jarabbawa saboda fitar tambayar da kuma amsar ta kafin shiga jarabbawar.
Mahalarta zanga-zangar sun yi ta rera taken yin alawadai da yanayin jagorancin Ma'aikatar.inda suke cewa kamata ya yi ma'aikatar ta samar da mafita domin kare hakin dubun dubatan daliban kasar ba wai ta soke jarrabawar ba.
Wannan rikicin ya samo asali ne tun bayan da wani ya watsa tambayoyin jarabbawar tare sakamakon a shafin yanar gizo na Facebook, inda kuma ya yi barazanar cewa matukar Gwamnati ba ta amsa bukatunsa ba zai ci gaba da watsa irin wannan lamari.
Daga cikin bukatun shine Gwamnati ta gaggauta biyan hakkokin malamai, da kuma soke shirin da ta billo da shi na shiga jami'a.