Alkahira ta gindya sharadi na dawo da alaka tare da birnin Ankara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7408-alkahira_ta_gindya_sharadi_na_dawo_da_alaka_tare_da_birnin_ankara
Kasar Masar ta gindaya sharadi na dawo da alakarta tare da kasar Turkiya
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jun 29, 2016 06:48 UTC
  • Alkahira ta gindya sharadi na dawo da alaka tare da birnin Ankara

Kasar Masar ta gindaya sharadi na dawo da alakarta tare da kasar Turkiya

Kakakin Ma'aikatar Harakokin wajen kasar Masar Ahmad Abu zaid ya sanar da cewa kasar sa ta na maraba da duk wani kokari da magabatan birnin Ankara ke yi na sake farfado da alaka tsakanin kasashe biyu.

Abu Zaid ya ce wajibi ne magabatan Turkiyan su mutunta juyin juya halin kasar na ranar 30 ga watan Yuni wanda shi ke tabbatar da an mutunta bukatun Al'ummar kasar.

A baya dai, Shugaban kasar na Turkiya Rajab Tayib Ordugan ya sanar da cewa sharadin farfado da alaka tsakanin kasar sa da Masar, sakin tsohon shugaban kasar Muhamad Mursi.

Alaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ne tun bayan juyin milkin da aka yiwa hanbararen shugaban kasar Muhamad Mursi a shekarar 2013.

Muhamad Mursi shine farkon shugaban kasar da aka zaba ta farkin Demokaradiya bayan faduwar Gwamnatin Husni Mubarak, da kuma yanzu haka yake ci gaba da fuskantar shara'a a kasar.