Bukatar Babban Malamin Al-Azhar na kafa kungiyar hadin kan Musulmi
Shugaban Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar ya bukaci kafa kungiyar hadin kan Al'ummar Musulmi
A cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan Alkhamis Shekh Ahmad Attayib Shugaban Jami'ar Al-Azhar ta Masar ya ce a halin da ake ciki bai zai yiyu aka kafa Gwamnatin musulinci ba a dukkanin kasashen musulmi to amma matasan musulmi na iya kafa kungiyar hadin kan musulinci.
Shekh Ahmad Attayib ya ce musulmi a kasashe daban daban ba su da sabani, kuma rashin sanya kasashe irinsu Malesiya da Indosiya a cikin kasashen musulmi saboda nisartar su daga gabas ta tsakiya kuskure ne.
Shugaban jami'ar ta Al-Azhar ya tabbatar da cewa gabatar da shawarar kafar kungiyar hadin kai a tsakanin kasashen musulmi kamar yadda aka kafa kungiyar tarayyar Turai abu ne mai yiyuwa, kuma Matasa ya kamata su yi kokari wajen tabbatar da wannan lamari.
Yayin da yake Ishara da Aya ta 55 cikin suratu Mumunun, Shekh Ahmad Attayib ya ce duk da irin sabani na yanki, ko babbancin launi, to amma a kwai wajibcin kiyaye hadin kai tsakanin Al'ummar musulmi saboda tuta guda ta hada mu wato ita ce ta Addinin Islama.