Rikici ya hallaka mutane da dama a tsakiyar Afirka
(last modified Tue, 05 Jul 2016 15:11:09 GMT )
Jul 05, 2016 15:11 UTC
  • Rikici ya hallaka mutane da dama a tsakiyar Afirka

Rikicin tsakanin tsofin 'yan tawayen saleka ya halaka mutane da dama a kudancin kasar Afirka ta tsakiya

Jami'an Jandarma na kasar Afirka ta tsakiya sun sanar a wannan talata cewa rikici tsakanin mayakan kungiyar UPC masu dauke da makamai da kuma suka kasance tsofin 'yan tawayen saleka ne a baya, ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 10 tare da jikkata wasu 25 na daban a garin Bambari dake kudancin kasar.

Sanarwar ta ce daga cikin wadanda rikicin ya ritsa da su har da fararen hula, kuma tuni Dakarun tsaro da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suka isa gurin da lamarin ya auku.

Tun a watan Decembar 2012 ne kasar Afirka ta tsakiya ta fada cikin rikici na kabilanci da addini, lamarin da ya yi sanadiyar faduwar Gwamnatin lokacin tare da asarar rayukan na dariruwan mutane bayan da wasu dubai suka bar mahalinsu.

Har yanzu Sabuwar Gwamnatin ta kasa tabbatar da tsaro kamar yadda ta yi alkawari bayan da ta samu nasarar jan ragamar milkin kasar.

A watan Maris din shekarar 2013 'yan tawayen saleka sun kwace iko da birnin Bangui saidai bayan shigar Dakarun kasa da kasa a farkon watan Avrilu na shekarar 2014, an yi waje da su.

Yanzu haka dai akwai Dakarun tsaro da sulhu na MDD kimanin dubu 12 a kasar.