Ziyarar Aikin Fira Ministan Kasar Indiya Zuwa Wasu Kasashen Afrika
A ziyarar aikin da fira ministan kasar Indiya zai gudanar a wasu kasashen Afrika, a cikin daren jiya Laraba ya isa birnin Maputo fadar mulkin kasar Mozambique, inda ya samu tarba daga mahukuntan kasar.
Rahotonni sun bayyana cewa: A ziyararsa da zai gudanar a kasar ta Mozambique fira ministan kasar Indiya Narendra Modi zai fi mai da hankali ne kan batun rattaba hannu kan yarjejeniyar sayan hatsi ne da nufin wadata miliyoyin al'ummar Indiya masu karamin karfi.
Har ila yau bayan kammala ziyarar aiki a kasar ta Mozambique, fira ministan Indiya zai kuma nausa zuwa kasashen Afrika ta Kudu, Tanzaniya da kuma Kenya. Rahotonnin sun kara cewa; Akwai hasashen cewa ziyarar Narendra Modi a wadannan kasashen Afrika guda hudu zai fi mai da hankali ne kan batun tattauna hanyoyin karfafa huddar kasuwanci a tsakaninsu musamman a bangaren makamashi, noma, taimakekkeniya kan harkar tsaro da sauransu.