An gurfanar da Shugaban kungiyar 'yar Jaridu a Masar
Kotun Hukunta manyan laifuka ta kasar Ta gurfanar da Shugaban kungiyar 'yan Jaridun kasar
Rahotanni daga birnin Alkahira sun ce a wannan Assabar kotun hukunta manyan laifuka ta gurfanar da Yahaha Falash shugaban 'yan jaridun kasar tare da wasu abokanin aikin sa biyu Jamal Abdulrahim da halid Bal'ashi da su ma gungu ne a cikin kungiyar.
Ana zarkin 'yan jaridun ne da laifin bada mafuka ga wasu 'yan jaridun da Gwamnati ke nema da suka hada da Amaru Badar da Mahmud Assaqa tare kuma da bayyana labaran karya dangane da harin da jami'an tsaro suka kai hedkotar 'yan jaridun dake birnin Alkahira.
An gudanar da Zaman kotun ne cikin kwararen matakan tsaro, inda rahoton ya ce Jami'an tsaro sun hana dukkanin 'yan jaridu shiga cikin harabar kotun.
Kafin hakan dai Jami'an 'yan sandan sun kai farmaki a cikibiyar kungiyar 'yan jaridun dake birnin Alkahira inda suka yi awan gaba da Amaru Badar da Mahmud Assaqa saboda sun bayyana adawarsu kan matakin Gwamnati na bayar da Tsibiran Tiran da Sanafir ga Masarautar Ali saoud.
Baya ga haka dubun dubutan 'yan kasar sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar gaba daya inda suka baiwa Ranar juma'ar kasa domin nuna adawa da wannan mataki da Shugaba Asese. a birnin Alkahira kadai an kame Mutane 22 a yayin zanga-zanga