Mahukuntan Masar Sun Hana Iyalan Shugaban Kungiyar Ihwan Ganawa Da Shi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7891-mahukuntan_masar_sun_hana_iyalan_shugaban_kungiyar_ihwan_ganawa_da_shi
Iyalan shugaban kungiyar Ihwanul-Muslim ta kasar Masar sun koka kan yadda mahukuntan kasar suka hana su ganawa da dan uwansu duk da cewa yana cikin mawuyacin hali sakamakon rashin lafiyar da ke fama da shi a gidan kurkuku.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 10, 2016 06:38 UTC
  • Mahukuntan Masar Sun Hana Iyalan Shugaban Kungiyar Ihwan Ganawa Da Shi

Iyalan shugaban kungiyar Ihwanul-Muslim ta kasar Masar sun koka kan yadda mahukuntan kasar suka hana su ganawa da dan uwansu duk da cewa yana cikin mawuyacin hali sakamakon rashin lafiyar da ke fama da shi a gidan kurkuku.

Kamfanin dillancin labaran Anatoliya na kasar Turkiyya ya habarta cewa: Iyalan Muhammad Badi'e shugaban kungiyar Ihwanul-Muslim ta kasar Masar sun dora alhakin duk wata matsalar tabarbarewar lafiyar dan uwansu kan mahukuntan Masar sakamakon hana su ganawa da shi a gidan kurkuku, kuma yau tsawon makonni uku suna gabatar da bukatar ziyarar dan uwan nasu amma an hana su ganinsa.

Wasu rahotonni sun bayyana cewa; Muhammad Badi'e yana fama da matsanancin rashin lafiya a gidan kurkukun da ake tsare da shi, kuma saboda da tabarbarewar lafiyar tashi har an kwantar da shi a asibiti.