Nijar Ta Bukaci A Kafa Rundunar Yaki Da Ta’addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8026-nijar_ta_bukaci_a_kafa_rundunar_yaki_da_ta’addanci
Shugaba Muhamadou Isufu na Jamhuriya Nijar ya nemi da a kafa wata rundunar soji don yaki da ta’addanci a kasashen Afirka ta Yamma da ke fuskantar barazanar kungiyar Boko Haram da mayakan Jihadi a Mali.
(last modified 2018-08-22T06:58:35+00:00 )
Jul 12, 2016 06:48 UTC
  • Nijar Ta Bukaci A Kafa Rundunar Yaki Da Ta’addanci

Shugaba Muhamadou Isufu na Jamhuriya Nijar ya nemi da a kafa wata rundunar soji don yaki da ta’addanci a kasashen Afirka ta Yamma da ke fuskantar barazanar kungiyar Boko Haram da mayakan Jihadi a Mali.

Yayin da ya ke jawabi wajen taron kwamitin jituwa na kasashen reno faransa wato Conseil de l’entente daya hada shugabannin kasashen Cote d’Ivoire da Benin da Burkina Faso da Togo a birnin Yammai, shugaba Isufu ya bukaci karfafa rundunar MDD ta MUNISMA da ke aiki a Mali don agazawa a duk lokacin da aka harin ta’addanci a Yankin.

Taron ya samu halartar shugaba Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire da Roch Marc Christian Kabore na Burkina Faso da Patrice Talon na Benin da Faure Gnassingne na Togo.