Nijar Ta Bukaci A Kafa Rundunar Yaki Da Ta’addanci
Shugaba Muhamadou Isufu na Jamhuriya Nijar ya nemi da a kafa wata rundunar soji don yaki da ta’addanci a kasashen Afirka ta Yamma da ke fuskantar barazanar kungiyar Boko Haram da mayakan Jihadi a Mali.
Yayin da ya ke jawabi wajen taron kwamitin jituwa na kasashen reno faransa wato Conseil de l’entente daya hada shugabannin kasashen Cote d’Ivoire da Benin da Burkina Faso da Togo a birnin Yammai, shugaba Isufu ya bukaci karfafa rundunar MDD ta MUNISMA da ke aiki a Mali don agazawa a duk lokacin da aka harin ta’addanci a Yankin.
Taron ya samu halartar shugaba Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire da Roch Marc Christian Kabore na Burkina Faso da Patrice Talon na Benin da Faure Gnassingne na Togo.