Nijar : Hukuncin Dauri Na Watanni 10 kan 'Yan Adawa 7
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8068-nijar_hukuncin_dauri_na_watanni_10_kan_'yan_adawa_7
Wata kotu a Yamai babban birnin Jamhuriya Nijar ta yanke hukuncin dauri na watanni 10 kan wasu 'yan adawa bakwai bisa samunsu da laifin tada zamne tsaye a lokacin tarben jagoransu Hama Amadu a ranar 14 ga watan Nowamba bara.
(last modified 2018-08-22T06:58:35+00:00 )
Jul 13, 2016 06:35 UTC
  • Nijar : Hukuncin Dauri Na Watanni 10 kan 'Yan Adawa 7

Wata kotu a Yamai babban birnin Jamhuriya Nijar ta yanke hukuncin dauri na watanni 10 kan wasu 'yan adawa bakwai bisa samunsu da laifin tada zamne tsaye a lokacin tarben jagoransu Hama Amadu a ranar 14 ga watan Nowamba bara.

Daga cikin mutanen da wanda hukuncin ya shafa harda tsohon ministan kiwan lafiya na kasar Soumana Sanda wanda shi ne babban sakatare na jam'iyyar adawa ta Moden Lumana.

Dama kafin wanan hukuncin 'yan adawa sun shafe kusan watanni takwas a gidan yari, wanda a cewar lauyarsu Mme Bary Bibata Niandou nan da 14 ga wtaan Agusta za'a iya sallamarsu.