An kashe wata tsohuwa Minista a Burundi
(last modified Wed, 13 Jul 2016 17:43:42 GMT )
Jul 13, 2016 17:43 UTC
  • An kashe wata tsohuwa Minista a Burundi

jami'an 'yan sandar Burundi sun sanar da kashe wata tsohuwar Minista kuma 'yar Majalisar dokokin kungiyar gabashin Afirka

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus daga birnin Bujunbura ya nakalto Jami'an 'yan sanda na cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wata tsofuwar ministan kasar mai suna Hafsa Mossi kuma ta kusa da shugaba Pierre Nkurunziza.

Marigayiyar ta kasance 'yar majalisar dokoki ta kasashen kungiyar gabashin Afirka tun daga shekarar 2012, kuma gungu ce a jam'iyyar da ke mulki a kasar.

Wasu 'yan bindiga ne guda biyu cikin mota a wata unguwar da ke a gabashin Bujumbura babban birnin kasar suka harbeta har lahira.

A nasa bangare Ministan harakokin wajen Ruwanda ya yi alawadai da yadda ake ake yi wa Jami'an Gwamnati kisan gilla a kasar ta Burundi.

Tun lokacin da aka fara tashin hankalin na Burundi a shekara bara, mayan sojoji da jami'an Gwamnati da dama aka kashe saboda ra'ayinsu na goyon bayan shugaba Pierre Nkurunziza wanda ya yi tazarce bayan wa'adin milkin sa ya kare a shekarar da ta gabata.

Har ila yau alkaluma sun ce sama da fararen hula 450 ne suka rasa rayukansu sannan kuma wasu dubai ne suka gudu daga cikin kasar sanadiyar tashin hankalin na bara.