Kasar Congo Zata Tura Wasu Sojojinta Zuwa Kasar Afrika ta Tsakiya
Kasar Congo Brazavile zata aiki da sojojinta zuwa kasar Afrika ta tsakiya.
Ministan harkokin wajen kasar Congo Brazaville ya bada sanarwan cewa kasarsa zata aiko ga sojojin kasar zuwa kasar Afrika ts Tsakiya. Charles Richard Mondjo ya bayyana haka a ne a jiya ya kuma kara da cewa sojojin sun sami horo na musamman don tabbatar da zaman lafiya a cikinn al'umma. Shafin yanar gizo na African Time ya ce sojojin zasu yi aiki ne karkashin sojojin majalisar dinkin duniya har zuwa lokacin da zasu kammala aikin nasu.
Har'ila yau labarin ya kara da cewa sojojin zasu yi aiki ne a birnin Bangi babban birnin kasar. Tun shekara ta 2013 ne kasar Afrika ta tsakiya ta fada cikin yakinnkabilanci da kum addini wanda ya kai ga rasa rayuka da kuma asarar dukiyoyi masu yawa. Har'ila yau miliyoyin mutanen kasar suna gudun hijira a cikin kasar ko kuma a wajenta.