Afirka Ta Tsakiya: Kin Amincewar Wata Kungiya Da Aje Makaman Yaki.
Kungiyar MPC mai dauke da makamai a kasar Afirka ta tsakiya ta ki amincewa da kwance damarar yaki.
Kungiyar MPC mai dauke da makamai a kasar Afirka ta tsakiya ta ki amincewa da kwance damarar yaki.
Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya ambato Abcar Sabone, mai magana da yawun kungiyar ta MPC yana fada a yau laraba cewa; Matukar ba a aiwatar da sharuddan tattaunawar sulhu ta kasa da aka yi ba, to ba za su taba aje makamansu ba.
Sabone ya ci gaba da cewa; Har yanzu kasar tana cikin rikici saboda haka dole ne kungiyoyi su ci gaba da rike makamansu.
Maganar ta Sabone dai ta zo ne a matsayin maida martani ga jawabin da shugaban kasar Fautin Archange Touadera ya yi na kwace makaman dukkanin kungiyoyi.
Tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a kasar ta Afirka ta tsakiya, an sami dawowar zaman lafiya na azo a gani.