Damuwar sace fararen hula A Kasar Afirka ta tsakiya
Kungiyoyin fararen hula sun sanar da sace Mutane kimanin 350 a kasar Afirka ta tsakiya
Kafar watsa labaran Afirka time ta habarta cewa a wannan Alkhamis wasu kungiyoyin fararen hula biyu Invisible Children da The Resolve a kasar Afirka ta tsakiya sun fitar da wani rahoto, inda suka ce a cikin watanni shida da suka gabata 'yan tawayen LRA sun sace fararen hula 344 a gabashin kasar, daga cikin su a kwai kananen yara 65.
Sanarwa ta kara da cewa ko baya ga wannan adadi a kwai wasu fararen hula 39 da ake tunanin 'yan tawayen sun sace ko kuma sun yi batan laya.
A nasa bangare, Mista Sean Poole, babban Darakta mai kula da tsare-tsaren kananen yara na MDD ya bukaci Kungiyoyin kasa da kasa da dauki matakan kare da kuma goyon bayan fararen hula, a kan cin zarafin 'yan tawaye.
Daga farkon wannan shekara ta 2016, Kungiyar 'yan tawayen LRA ta kai hare-hare 122 a gabashin Afirka ta tsakiya da kuma arewacin D/Congo tare da yin awan gaba da fararen hula 498.