Iran : Zarif, Zai Fara Ran-gadi A Yammacin Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8542-iran_zarif_zai_fara_ran_gadi_a_yammacin_afrika
A wannan lahadin ce ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif zai fara wani ran-gadi na kwanaki shida a yammacin Afrika.
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 23, 2016 10:22 UTC
  • Shugaba Piere Nkurinziza da ministan harkokokin wajen Iran a wata ziyara Mr Zarif a Burundi a cikin shekara 2015
    Shugaba Piere Nkurinziza da ministan harkokokin wajen Iran a wata ziyara Mr Zarif a Burundi a cikin shekara 2015

A wannan lahadin ce ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif zai fara wani ran-gadi na kwanaki shida a yammacin Afrika.

A wannan ran-gadin Mr Zarif zai kasance tare da rakiyar wata babbar tawagar 'yan kasuwa da 'yan siyasa na kasar Iran.

Ana sa ran Mr Zarif zai Ghana da shugabannin kasa, da shugabannin majalisar dokoki da ministoci na wasu kasashen yankin da suka hada da  Najeriya, Ghana, Guinea Konacry da kuma Mali a cewar kanfanin dilnacin labaren kasar na IRNA.

Wannan dai zai kasance ran-ganin na Mr Zarif irin sa na uku a nahiyar Afrika, inda a ran-gadinsa sa na farko a shekara 2015 ya ziyarci wasu kasashen gabashin Afrika da suka hada da Kenya, Uganda, Burundi da kuma Tanzaniya.