Kirar Azhar ta Masar kan kusanci da hadin kan Mazhabobin Musulinci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8572-kirar_azhar_ta_masar_kan_kusanci_da_hadin_kan_mazhabobin_musulinci
Jami'ar Al-azhar ta Masar ta bukaci samar da kusanci tsakanin Mazhabobin Addinin musulinci
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 24, 2016 06:52 UTC
  • Kirar Azhar ta Masar kan kusanci da hadin kan Mazhabobin Musulinci

Jami'ar Al-azhar ta Masar ta bukaci samar da kusanci tsakanin Mazhabobin Addinin musulinci

Shugaban Jami'ar Al-Azhar kuma babban mai bada fatawa na kasar Masar Ahmad Attayib ya bukaci Dukkanin manya maluman Addinin islama sunna da shi'a da su bayar da fatawa da haramcin kisan da ake yiwa Al'ummar musulmi a Duniya, inda za ka samu mabiya suna suka kashe 'yan shi'a ko kuma 'yan shi'a su kashe 'yan sunna.

Attayib ya ce Al-Azhar na bukatar samun kusanci tsakanin Mazhabobin Addinin Musulinci musaman ma tsakanin mazhabobi shi'a da Sunna domin yin hakan na da mahimancin gaske a tsakanin Al'ummar musulmi.

Har ila yau Attayib ya ce bai kamata wasu su rike banbanci mazhaba a matsayin wata hanyar ta tashin hankali, kuma a halin da ake cikin a kwai kafafen sadarwa da dama da suke watsa ababe dake kara hura wutar rikici a tsakanin mazhabobbin Addinin musulmi, masu irin wadanda aiyuka ba sa kaunar kawo karshen tashin hanhali da zubar da jinin bayin A... da ba su ji ba su gani ba.