Kotu Ta Daure Madugun Yan Adawar Conco Brazzaville Shekaru Biyu A Kurkuku
Kotu a kasar Congo Brazzaville ta zartar da hukuncin daurin tsawon shekaru biyu a gidan kurkuku kan madugun 'yan adawar kasar kan zargin kunna wutan rikici a kasar.
Kotu a kasar Conco Brazzaville ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kurkuku tare da biyan tara na kudi kimanin Euro 3,800 kan madugun 'yan adawar kasar Paulin Makaya kan zargin hannu a shirya zanga-zanga a kasar bada izini ba a shekara ta 2015.
Tun a ranar 23 ga watan Nuwamban shekara ta 2015 ne jami'an tsaron kasar Congo Brazzaville suka kame Paulin Makaya shugaban jam'iyyar Unis Pour le Congo {UPC} a takaice kan zargin laifin halattar zanga-zangar lumana da al'ummar kasar suka gudanar a cikin watan Oktoban shekara ta 2015 domin nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin Congo Brazzaville na yin kwaskwarima wa kudin tsarin mulkin kasar.
Lauyoyin da suke kare Paulin Makaya gami da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International sun yi Allah wadai da wannan hukunci tare da bayyana cewa babu adalci a cikinsa ko kadan.