Sheikhul Azhar: Dole Ne Malamai Su Haramta Rikicin Sunnah Da Shi’a
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8677-sheikhul_azhar_dole_ne_malamai_su_haramta_rikicin_sunnah_da_shi’a
Babban malamin cibiyar mulunci ta mazhabobin sunnah mafi girma a duniya ta Azahar da ke kasar Masar ya bukaci malamai na dukkanin bangarorin sunnah da shi’a da su fitar da fatawa ta haramta rikici a tsakanin bangarorin biyu.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 26, 2016 02:11 UTC
  • Sheikhul Azhar: Dole Ne Malamai Su Haramta Rikicin Sunnah Da Shi’a

Babban malamin cibiyar mulunci ta mazhabobin sunnah mafi girma a duniya ta Azahar da ke kasar Masar ya bukaci malamai na dukkanin bangarorin sunnah da shi’a da su fitar da fatawa ta haramta rikici a tsakanin bangarorin biyu.

Shafin yada labarai na Al'anba daga kasar Kuwait ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Ahmad Tayyib a lokacin da yake amsa tambayoyin maneama labarai ya bayyana cewa, babu wani dalilin da zai sanya bangarorin musulmi na shi’a da sunnah su yi rikici da juna, domin kuwa dukkanin su musulmi ne a hukunci na muslunci domin dukkaninsu sun sheda kalmomi biyu na shahada.

Ya ce cibiyar Azhar za ta ci gaba da yin kokari domin ganin an samu daidaiton fahimta a kan kana binya hada musulmi shi’a da sunna, sauran abubuwan da ake da sabani a kansu na fikihu da sauran batutuwa na ilimi, wannan lamari ne da ya shafi malamai, kuma za a iya samun mafita ta yadda kowa zai rike fahimtarsa da aka samu sabani a kanta, amma a yi aiki tare a kana bin da ya hada dukkanin bangarorin musulmi.

Shehin malmin ya ce yanzu haka ya umarci manyan malaman cibiyar Azahar da su zauna su fitar da fatawa ta haramta rikici ko kafirta juna tsakanin ‘yan sunnah da ‘yan shi’a, domin kuwa an yi manyan malamai a wanann cibiya ta Azahar na shi’a da sunna fiye da shekaru dubu da suka gabata, amma Azhar ba ta san da wani rikci makamancin haka ba sai a wannan zamani.

Malamin ya ce akwai wasu ‘yan tsiraru a cikin dukkanin bangarorin biyu na sunnah da shi'a da suke ruruta wannan wutar rikici ta fitina, wanda nauyi ne da ya rataya kan manyan malamai na sunnah da shi’a su kawo karshen haka, ta hanyar fitar da fatawoyi na wajabcin hadin kai da nisantar rikici da kafirta juna a tsakanin dukkanin musulmin da ya yi kalmar shahada, wanda shi ne ma'auni na muslunci.