Iran Ta Bukaci Karfafa Hulda Tsakanin Bankunanta Da Na Kasar Ghana
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da manya manyan jami'an gwamnati a kasar Ghana
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana bukatar karfafa huldan bankuna tsakanin kasarsa da Kasar Ghana. Zarif ya bayyana haka ne a yau talata a binrin Acra babban binrnin kasar ta Ghana inda ya fara ziyarar aiki tun jiya Litinin. Ministan ya kara da cewa ya na tare da tawagar iraniyawa yan kasuwa a ziyarar tasa kuma bai ga wani dalili da zai hana bunkasa dangantakar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Ghana ba.
Kafin haka dai Ministan ya ghana da shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama inda bangarorin biyum suka tattauna yadda zasu yi aiki tare a cikin kungiyoyin kasa da kasa da kuma yaki da ayyukan ta'addanci.
Har'ila yau Mohammad Zarif yana gana da shugaban majalisar dokokin kasar ghana Edward Doe Adjaho inda suka jadda bukatar aiki tare da kara dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Kasar Ghana ce zanga Mohammad Zarif da tawagarsa a ziyarar kasashe hudu da zai ziyata a Nahiyar Afrika a wannan karon. A jiya ne ministan ya ziyarci Nigeria sannan ana saran daga kasar Ghana zai je kasashen Guiner Conakry da Mali.