Kasashen Niger Da Aljeriya Sun Jaddada Muhimmancin Karfafa Alaka A Tsakaninsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8740-kasashen_niger_da_aljeriya_sun_jaddada_muhimmancin_karfafa_alaka_a_tsakaninsu
Gwamnatocin kasashen Niger da Aljeriya sun jaddada muhimmancin karfafa alaka da taimakekkeniya a tsakaninsu da nufin bunkasa ci gaban kasashen biyu.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 27, 2016 01:14 UTC
  • Kasashen Niger Da Aljeriya Sun Jaddada Muhimmancin Karfafa Alaka A Tsakaninsu

Gwamnatocin kasashen Niger da Aljeriya sun jaddada muhimmancin karfafa alaka da taimakekkeniya a tsakaninsu da nufin bunkasa ci gaban kasashen biyu.

A ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Niger Ibrahim Yakuba da takwararsa na kasar Aljeriya Ramtane Lamamra a birnin Alges fadar mulkin kasar Aljeriya a jiya Talata: Ministocin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi alakar kasashen biyu tare da jaddada muhimmancin karfafa alakar jakadanci da taimakekkeniya a tsakaninsu musamman kan batun yaki da ta'addanci.

A ganawarsa da manema labarai ministan harkokin wajen Jamhuriyar Niger Ibrahim Yakuba ya bayyana cewa: Barazanar ayyukan ta'addanci da matsalar bakin haure suna daga cikin matsalolin da suke addabar kasashen Niger da Aljeriya. 

Tun a shekara ta 2010 kasashen Mauritaniya, Niger, Mali da Aljeriya suka cimma yarjejeniyar hadin gwiwa a fagen fuskantar matsalolin tashe-tashen hankula da barazanar ta'addanci a tsakaninsu.