Kashe 'yan ta'adda A Kasar Masar
Sojojin Masar Sun Kashe 'Yan ta'adda Masu Yawa A Kasar Masar
Majiyar Tsaron Masar ta ce; Sojojin Kasar sun kashe 'yan kungiyar ta'adda ta "Ansaru Baitul-Muqaddas" masu yawa a yankin Sina ta arewa.
Tashar telbijin din al-mayadeen daga kasar Lebanon ta nakalto sojojin Masar suna fadar cewa; farmakin da su ka kai a yankin Rafah ta yamma, yayi sanadin kashe 'yan kungiyar "Ansarul-Baitul-Muqaddas" 25 tare kuma da jikkata wasu 15.
Majiyar sojan Masar din ta ci gaba da cewa; An yi amfani da jirage masu saukar angulu samfurin Apache a kan 'yan ta'addar da su ke a garin Bal'aa a Rafah ta yamma.
A ranar litinin din da ta gabata an kai wani harin ta'addanci a yankin na Rafah wanda ya dauki rayukan jami'an tsaron Masar 11.