Nijar : Matsalar Kudi, Na Barazana Ga Aikin Samar Da Abinci
Hukumar samar da tallafin abinci ta MDD wato PAM, ta yi gargadin cewa karancin kudi na iya dakatar da aikin ta na yaki da matsalar karamcin abinci mai gina jiki ga yara kanana a Jamhuriya Nijar.
Hukumar ta ce sanadin hakan aikin ta na iya tsayawa daga nan zuwa watan Satumba a wannan kasa inda dubban yara kanana ke fama da matsalar ta kamamcin abunci mai gina jiki.
Kakakin offishin hukumar a Yamai babban birnin jamhuriya ta Nijar, Vigno Hounkanli ya shaidawa kanfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa tuni suka rage yawan abuncin da suke baiwa mabukatan.
hukumar ta PAM ta ce tana bukatar tallafin kudi da yawan su ya kai kusan miliyan ashirin da daya da rabi, domin tallafawa al'umma ta Nijar mabukata daga watan Satumba zuwa Desamba mai zuwa.
Wasu Alkaluma da hukumar kiwan lafiya ta duniya ta fitar sun nuna cewa a Nijar matsalar tamowa ta kai kashi 15%, wanda tuni ya kai mizanin da ake bukatar agajin gaggawa.