Gwamnatin Nijer ta tsawaita dokar ta bace a Jihar Difa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8899-gwamnatin_nijer_ta_tsawaita_dokar_ta_bace_a_jihar_difa
A jumhoriyar Nijer, Gwamnati ta tsawaita dokar ta bace na watani uku a Jihar Difa dake kudu maso gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Jul 30, 2016 14:37 UTC
  • Gwamnatin Nijer ta tsawaita dokar ta bace a Jihar Difa

A jumhoriyar Nijer, Gwamnati ta tsawaita dokar ta bace na watani uku a Jihar Difa dake kudu maso gabashin kasar

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana karin watanni uku a dokar ta baci da aka sanya a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar mai fama da rikicin kungiyar ta'addancin nan ta  Boko Haram.

Hare-haren mayakan na kungiyar Boko Haram din da ya yi tsanani a wannan Mayun da ya gabata ya yi sanadiyar gudun hijra na duban mazauna gariruwn Bosso da yebi dake kan iyaka da Najeriya a yankin tafkin Chadi,nda ya zuwa yanzu mutane dubu 69 ne suka kaurace wa muhallansu a wannan yanki kamar yadda sashin kula da agaji na al'umma a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a wani rahoto da ya fitar a ranar Juma'a.

 . Yanzu dai wannan dokar tabaci a yankin na Diffa za ta kai har ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa,

A watan favrayun da ya gabata ma Gwamnatin ta Nijer ta tsawaita dokar ta bace a yankin na Diffa