Zanga-Zangar 'yan burundi a gaban Ofishin Jakadancin Faransa
Kafafen watsa Labaran Burundi sun sanar da zanga-zangar a gaban ofishin Jakadancin Faransa dake birnin Bujunbura
Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto Kafafen watsa labaran kasar Burundi na cewa Kimanin Mutane dubu guda ne suka taru a gaban ofishin jakadancin Faransa dake birnin Burundi a wannan Assabar domin nuna adawarsu da wani kudiri na Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kasar Faransar ta gabatar wanda ya bada damar tura Dakarun wanzar da zaman Lafiya na Majalisar 228 a kasar.
Kafafen watsa labaran Kasar sun ce masu adawa da wannan kudiri sun fara jerin gwanon ne daga dandalin 'yanci na birnin Bujunbura zuwa Ofishin jakadancin Kasar Faransa dake birnin inda suke rera taken alawadai da Gwamnati Faransa tare kuma da bayyana adawar su da aika Dakarun wanzar da zaman Lafiya na Majalisar dinkin Duniya zuwa cikin kasar.
Mahalarta zanga-zangar sun ce manufar aikewa da Sojojin wata kasa cikin kasar kisan killa kamar yadda ya faru a shekarar 1994 a kasar Ruwanda.