Tarayyar Afirka ta kafa sharadin aikewa da dakarun sulhu zuwa kasar Burundi.
(last modified Mon, 01 Feb 2016 18:02:09 GMT )
Feb 01, 2016 18:02 UTC
  • Tarayyar Afirka ta kafa sharadin aikewa da dakarun sulhu zuwa kasar Burundi.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa; Amincewar gwmanatin kasar Burundi shi ne sharadin aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa kasar.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato kwamitin sulhu da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirkan yana cewa; ya aike da tawaga zuwa kasar Burundi domin gasmar da gwmnati ta amince da karbar dakarun tabbatar da zaman lafiya.

Kwamitin Sulhu da zaman lafiyar na kungiyar tarayyar Afirkan ya bijiro da aniyarsa ta aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya 5000, zuwa kasar Burundi, sai dai gwamnatin kasar ta ki amincewa.

A bisa dokokin tarayyar Afirka za a aiwatar da batun aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiyar ne a kasar da ta ke fama da rikici bisa amincewar gwmanatin kasar ko kuma ba da amincewara ba, bisa yadda hali ya bada.

Kasar ta Burundi dai ta fada cikin rikice ne tun bayan da shugaba Peer Nkurunziza ya yi tazarce.