'Yan Gudun hijirar Burundi Sun Koma Gida Daga Tanzania
Gwamnatin Burundi ta Sanar Da Komawar 'yan gudun hijirar da su ka nemi mafaka a Tanzania.
Kafar watsa labarun Africa Time; ta nakalto kantoman gundumar Cankuzo da ke arewa maso gabacin kasar, ta Burundi, Njiji Desire yana cewa; Iyalai 70 na Burundi da su ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira na ( NDUTA) a kasar Tanzania sun koma gidajensu a yankin Mishiha.
A can kasar Tanzania ma an sanar da komawar iyalai 70 da su ka kunshi mutane 157 zuwa gida.
Gwamnatin kasar ta Burundi tana nuna jin dadinta akan yadda 'yan kasar da su ke zaman gudun hijira su ke komawa gida.
Kungiyar bada agaji ta duniya Red Cross ta bude wata kafa ta bada dama ga 'yan gudun hijirar da su koma gida.
Fiye da shekara guda kenan mutanen kasar Burundi suka fara fita gudun hijira saboda rikicin da ya biyo bayan tazarcen shugaba Pierre Nkurunziza.