Sharhi : Dakarun Masar Sun Halaka Jagoran Kungiyar Ansar Bait Maqdis
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9181-sharhi_dakarun_masar_sun_halaka_jagoran_kungiyar_ansar_bait_maqdis
A jiya ne rundunar sojin kasar Masar ta sanar da kashe Abu Du'a Ansari jagoran kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah ta Ansaru Bait Maqdis, a wani harin ba zata da aka kai a maboyarsa acikin yankin Sinai da ke kudancin kasar ta Masar.
(last modified 2018-08-22T06:58:43+00:00 )
Aug 05, 2016 00:54 UTC
  • Sharhi : Dakarun Masar Sun Halaka Jagoran Kungiyar Ansar Bait Maqdis

A jiya ne rundunar sojin kasar Masar ta sanar da kashe Abu Du'a Ansari jagoran kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah ta Ansaru Bait Maqdis, a wani harin ba zata da aka kai a maboyarsa acikin yankin Sinai da ke kudancin kasar ta Masar.

Kakakin rundunar sojin kasar Masar Janar Muhammad Samir ne ya sanar da hakan a jiya, inda ya ce an kaddamar da wannan farmaki ne na hadin gwiwa tsakanin sojojin sama da na kasa da ke karkashin rundunar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar Masar, wanda kuma a cewarsa hakan ya yi sanadiyyar mutuwar jagoran 'yan ta'adda na Ansaru Bait Maqdis Abu Du'a Ansari da kuma dukkanin masu tsaron lafiyarsa, kamar yadda kuma aka kasha wasu mayakn kungiyar 45 tare da jikkata wasu fiye da 100, tare da rusa rumbunan ajiye makamai na kungiyar.

Kungiyar ta bayyana ne da karfinta bayan kifar da tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Mursi na kungiyar 'yan uwa musulmi a cikin watan Yulin 2013, daga bisani kuma ta sanar da yankin Sinai a matsayin yankin da take iko da shi.

Kungiyar dai ta dauki alhakin kaddamar da hare-hare a kasar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutuwar daruruwan sojoji da 'yan sanda, kamar yadda kuma sun kashe mutanen gari da dama, musamman a cikin yankin na Sinai, inda sukan kashe duk wanda suka zarge shi da cewa yan ada alaka da gwamnatin kasar ta Masar.

A cikin watan Nuwamban shekara ta 2014 kungiyar ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah wahabiyyah ta ISIS, inda ta koma babban reshen kungiyar ta ISIS a kasar Masar.

Baya ga kai hare-hare kan jami'an tsaron Masar da kuma fararen hula na kasar,a  cikin watan Oktoban shekarar 2015 da ta gabata kungiyar ta harbor wani jirgin fasinja na kasar Rasha, inda suka kasha masu yawon bude 224 dukkaninsu 'yan kasar Rasha.

Kasar Masar dai na zargin gwamnatin kasar Qatar da daukar nauyin wannan kungiya, kasantuwar kungiyar ta alakanta kanta da hambarar da gwamnatin Mursi, wanda dan kungiyar 'yan uwa musulmi ne kungiyar da gwamnatin kasar Qatar ke sahun gaba wajen daukar nauyinta, bugu da kari hakan hadewar kungiyar da kungiyar ISIS, wadda kasar Qatar ke kan gaba wajen daukar nauyinta tare da wasu kasashen larabawa daidai da maslaharsu ta siyasa, kamar yadda suke yi a Syria da Iraki da kuma Yemen da Libya.

Ko shakka babu halaka Abu Du'a Ansari jagoran 'yan ta'addan takfiriyya wahabiya na Ansaru Bait Maqdis da sojojin masar suka yi, babbar nasara ce a gare su ta fuskar tsaro, kamar yadda hakan kuma yake nasara ce ta fuskar siyasa ga shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi, wanda da dama daga cikin al'ummar kasar suke kallon cewa ya gaza ta fuskoki da dama, musamman ta fuskar tsaro, inda dakarun kasar suka kasa daike wannan kungiya ta 'yan ta'adda da ta addabi al'ummar kasar ta Masar.