An Kama manyan Jami'an tsaron Kasar Turkiya 4 A Arewacin Masar
Dakarun tsaron Masar sun kame wasu manyan jami'an tsaro na Ma'aikatar leken asirin kasar Turkiya 4 a tsibirin Arewacin kasar
Jami'an tsaron Turkiyan da aka kame a arewacin kasar Masar din sun hada da Isma'il Ali Bal, Diya'uddin muhamad Odu, Bakush Alhusain gami da Abdul... Alhusaini.
Majiyar kasar Masar din ta ce Jami'an leken asirin Turkiyan da aka kame na taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda ne a arewacin kasar, tun bayan juyin milkin da aka yiwa zababben shugaban kasar na farko ta hanyar Democradiya Muhamad Mursi, aka samu billar kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar Masar din daga cikin su a kwai kungiyar Ajnadu Masar da Kungiyar Wulayatu Sinai.wanda ta yi mubaya'a da Kungiyar IS a shekarar 2014.
Daga Lokacin da aka yiwa Shugaba Mursi juyin milki a tsakiyar shekarar 2013 zuwa yanzu dariruwan Sojoji da 'yan sanda ne suka rasa rayukansu sanadiyar harin masu tayar da kayar bayan na yankin Sinai dake arewacin kasar.