Dubban Mutanen Kasar Burundi Ne Suka Yo Hijira Zuwa Kasar Tanzania
Gwamnatin kasar Tanzania ta bayyana cewa mutanen kasar
Gwamnatin kasar Tanzania ta bayyana cewa mutanen kasar Burundi kimani dubu 130 ne suka sami mafaka a kasar sanadiyyar rikicin cikin gida da Burindi take fama da shi.
Kamfanin dillancin labaran Chihuwa na kasar China, ya nakalto Isaac Nantanga kakakin ma'aikatar cikin gida na kasar Tanzania yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa an tsugunar da yan gudun hijiran ne a sansanoni guda biyu, sannan gwamnatin kasar tana samun tallafi daga hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya wajen kula da yan gudun hijirar. Nantanga ya kara da cewa tun watan Afrilun shekarar ta 2015 ya zuwa yanzu yan gudun hijira daga kasar Burundi 130,000 suka shiga kasar kuma yawansu na karuwa a ko wace rana. Banda Burundi dai kasar Tanzaia tana karban bakoncin yan gudun hijira daga kasashen Dmr. Congo da kuma Somalia.