Masar A Shirye Take Da Bada Gudumawar Soje Ga Kawayenta Na Larabawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i937-masar_a_shirye_take_da_bada_gudumawar_soje_ga_kawayenta_na_larabawa
Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi ya bayyana cewa
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 18, 2016 02:25 UTC
  • Masar A Shirye Take Da Bada Gudumawar Soje Ga Kawayenta Na Larabawa

Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi ya bayyana cewa

Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta aika da sojojinta zuwa ko wace kasa daga cikin kasashen larabawa wadanda suke kawance da su idan sun bukaci hakan. Kamfanin dillancin labaran IRNA ya ce ya sami labari daga wata kafar yada labarai na kasar kuwait tana cewa, a wani ganawan da shugaba Abdul Fatah Sisi ya yi da wata jaridr Kuwait ta yi da shi a jiya Laraba, shugaban ya ce duk wata kasar larabawa wacce tace kawance da itsa sojojin kasarsa a shirye take ta tallafa mata da su.

Kasar Masar dai ce kasar larabawa wacce ta fi ko wannensu yawan mutane. amma don lalacewar tattalin arzikin kasar tana karban tallafin daga kasashen larabawa na bakin tejun farisa ne.

A yakin da kasar saudia ta shiga a kasar Yemen dai masar bayyana goyon bayanta da yakin ta kuma yi alkawar aike da sojojinta zuwa kasar ta Yemen don talafawa saudia amma har yanzun hakan bai faruba.