Mutane 14 Suka Mutu Sakamakon Ambaliya Ruwa A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9526-mutane_14_suka_mutu_sakamakon_ambaliya_ruwa_a_nijar
Gwamnatin Nijar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa mutane 14 ne suka rasa rayukansu kana wasu 46,296 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliya ruwa da aka samu a sassa daban daban na kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 12, 2016 10:18 UTC
  • Mutane 14 Suka Mutu Sakamakon Ambaliya Ruwa A Nijar

Gwamnatin Nijar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa mutane 14 ne suka rasa rayukansu kana wasu 46,296 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliya ruwa da aka samu a sassa daban daban na kasar.

Akasarin wadanda lamarin ya rusa dasu yara ne wadanda ruwa ya ci, ko kuma gidaje suka rufta masu.

Haka zalika an samu barna mai yawa data shafi wuraren kiwo da kuma filayen noma, inda kuma aka samu hasara dabbobi manya da kanansu da yawansu ya kai 19,536. 

Sanarwa da aka fitar a gidan talabijin din kasar ta ce lamarin ya fi shafar jihohin Tawa dake yammaci da kuma Agadas dake arewaci duka a hamada yankin Sahel inda ba'a saba ganin irin hakan ba.

Tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da aikewa da tallafi abinci na tonne 362 ga wadanda lamarin ya shafa, kana ta ce ana cikin shirin aikewa da wani tallafin wanda ba na abinci ba tare da tallafin abokan huldar ta.